Connect with us

Firstpost

Tinubu zai ƙaddamar da shirye-shiryen rage tsadar rayuwa a makonni masu zuwa

Tinubu zai ƙaddamar da shirye-shiryen rage tsadar rayuwa a makonni masu zuwa

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da wasu shirye-shiryen rage raɗaɗin tsadar rayuwa a makonni masu zuwa.

Shettima ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Legas.

Ya ce cikin shirye-shiryen da za a ƙaddamar akwai baburan adaidaita sahu masu amfani da lantarki 10,600 a Arewa maso Gabas, da kuma motocin bas 300 da tasi na dijital, domin rage kuɗin sufuri da nauyin da ke kan ’yan ƙasa.

“A cikin makonni masu zuwa, za mu ƙaddamar da shirin jigilar dijital a Arewa maso Yamma. Za mu ƙaddamar da adaidaita sahu mai lantarki 10,600 domin rage raɗaɗin mutane a Arewa maso Gabas, da kuma motocin bas 300 da tasi na dijital,” in ji shi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce gwamnatin ta fahimci irin matsin da ’yan Najeriya ke fuskanta sakamakon matakan tattalin arzikin da aka ɗauka, amma ya ce “lokacin matsi ba ya tabbata har abada”.

“Mun san da wahalar da ’yan Najeriya ke sha, amma lokacin matsi ba ya tabbata har abada; mutane masu juriya ne ke ɗorewa,” in ji Shettima.

Ya kuma ce Shugaba Tinubu na “tausaya wa talaka”, yana mai cewa shirye-shiryen da gwamnati ke shirin ƙaddamarwa na daga cikin matakan da za su taimaka wajen sauƙaƙa rayuwar jama’a.

Da yake kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin, Shettima ya ce Najeriya tana dab da durƙushewar tattalin arziki lokacin da gwamnatin Tinubu ta karɓi mulki.

Ya ce kuɗin ajiyar ƙetare na ƙasar bai kai dala biliyan 3.9 ba a lokacin, wanda ya ce bai isa a shigo da man fetur na tsawon wata guda ba.

Shettima ya ce Shugaba Tinubu ya ɗauki mataki na “ƙarfin hali” wajen cire tallafin man fetur da kuma daidaita kasuwar canjin kuɗi.

“Tattalin arzikin na daf da durƙushewa. Ya ceci tattalin arzikin. Ya ceci ƙasar daga wargajewa,” in ji shi.

Ganawar Shettima da Tinubu a Legas ita ce karon farko da suka bayyana tare tun bayan dawowar shugaban ƙasar daga hutunsa a Turai, da kuma dawowar mataimakin shugaban ƙasar daga Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a New York.

Tinubu ya ce a wani jawabin da ya yi yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai cewa ƙasar na kan hanyar samun wadata.

Sai dai jagororin adawa, Atiku Abubakar na ADC da Peter Obi na NDC, sun soki wannan iƙirari.

Atiku ya zargi gwamnatin da jefa ’yan Najeriya cikin matsanancin talauci tun bayan hawanta mulki a 2023, yayin da Obi ya ce ’yan ƙasar na fuskantar matsananciyar yunwa da rashin tsaro.

Continue Reading
You may also like...

More in

Recent Post

Advertisement Enter ad code here

Facebook

Headlines

To Top