Lakurawa sun kashe ɗan sa-kai a wani sabon hari a Sakkwato
Ana zargin Lakurawa sun kashe mutane biyu, ciki har da wani jami’in sa-kai, a ƙauyen Ungushi da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe a Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin garin ya kuma samu raunin harbin bindiga a yayin harin da ya faru a yammacin Lahadi.
- ’Yan bindiga sun bai wa iyalan masu yi wa ƙasa hidima wa’adin biyan N1bn kuɗin fansa
- Duk mai muƙamin da ke jin bai amfana da gwamnatina ba ya yi murabus — Lawal
Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun shiga ƙauyen tare da bude wa mutane wuta.
Hakan ya sa jami’an sa-kai suka yi musayar wuta da ta ɗauki sama da awa guda.
Wani jami’in tsaro ya ce an tura sojoji, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa ƙauyen bayan samun labarin harin.
“Mun dawo daga ƙauyen ne yanzu. Muna samun labari, aka tura sojoji, jami’an tsaron al’umma da ’yan sanda zuwa ƙauyen, amma ’yan ta’addan sun riga sun tsere kafin mu isa,” in ji shi.
Majiyar ta ce waɗanda aka kashe sun haɗa da wani manomi da ke dawowa daga gonarsa da kuma wani jami’in sa-kai.
An kai mutumin da ya samu rauni asibiti domin yi masa magani.
Haka kuma, akwai rahotannin cewa an kashe ’yan ta’adda uku yayin musayar wutar, amma majiyar ta ce ba za ta iya tabbatar da hakan da kanta ba.
“Ina ganin sun ji cewa jami’an tsaro na zuwa ne, shi ya sa suka tsere. Amma jami’an sa-kai sun samu damar fatattakar su bayan sun yi musayar wuta mai tsanani,” in ji shi.
Harin ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan ayyukan Lakurawa da sauran ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a wasu al’ummomin da ke kusa da iyakokin Jihar Sakkwato.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da harin, amma ya ce yana jiran ƙarin bayani daga jami’in ’yan sandan yankin da abin ya shafa.