Kotu ta sake ɗage shari’ar waɗanda suka kitsa harin Yelwata
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Binuwai, ta dakatar da shari’ar waɗanda suka kitsa kashe mutane 200 a garin Yelwata da ke Ƙaramar Hukumar Guma.
Hakan ya biyo bayan roƙon da lauyan da ke kare waɗanda ake tuhuma ya yi na neman ɗage shari’ar saboda bai kammala nazarin muhimman bayanai a kan shari’ar ba.
- Tsohon Kwamishinan kuɗi na Kano, Farfesa Kabiru Dandago, ya rasu
- Dakatar da Sheikh Alƙali Zariya kan sukar Tinubu ya tayar da ƙura
A baya dai alƙalin kotun, Joyce Abdulmalik, ya ɗage shari’ar ne bayan lauyan mutum na takwas da na tara daga cikin waɗanda ake zargi da Y.A Hassan ya bayar da uzurin cewa zaman ne na farko da aka yi da shi, tare da neman kotun ta ba shi lokaci domin nazarin zargin da ake yi wa waɗanda yake karewa.
Aminiya ta ruwaito yadda rundunar tsaron DSS ta kama mutum tara da ake zargi a ranar 2 ga watan Fabrairu, bayan shugaba Tinubu ya bayar da umarnin yin hakan, bisa zarginsu da kisan mata da ƙananan yara a ranar 13 ga watan Yunin 2025.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Ardo Lawal Mohammed Dono, Ardo Muhammadu Saidu, Alhaji Haruna Abdullahi.
Sauran sun haɗa da Yakubu Adamu Musa Mohammed, Abubakar Adamu, Shaibu Ibrahim, Sale Mohammed, da Bako Jibrin.