Connect with us

Firstpost

Iran ta ce ƙarfin soji ba zai kawo wa Amurka mafita ba

Iran ta ce ƙarfin soji ba zai kawo wa Amurka mafita ba

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce ci gaba da amfani da ƙarfin soji ko ƙarin takunkumi ba zai kawo wa Amurka wata mafita ta ganin ƙarshen rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Araghchi ya ce mafita guda ita ce tattaunawa da za a gudanar bisa doron adalci, mutunci da diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin da kuma abin da ya kira hare-haren da aka kai wa Iran.

Kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA, ya ruwaito ministan yana bayyana hakan ne ranar Lahadi, yayin da yake tattaunawa da jakadu da jami’an diflomasiyyar ƙasashen waje da ke Tehran.

“Mafita ɗaya tilo ita ce wacce za a samu ta hanyar tattaunawa, bisa adalci da gaskiya, tare da mutunci da diflomasiyya,” in ji shi.

Araghchi ya ce idan Amurka ta sake komawa amfani da ƙarfin soja, Iran a shirye take ta ɗauki duk matakan da suka dace domin kare kanta.

Ya ce Tehran na fatan Washington za ta zaɓi hanyar tattaunawa maimakon ci gaba da gwabza yaƙi.

Ya kuma ce Iran ta sha fuskantar matsin lamba daga Amurka, sai dai ya bayyana cewa ƙarin takunkumi ba zai warware rikicin ba.

Jawabin na Araghchi na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a Mashigar Hormuz, hanyar da ke da muhimmanci wajen safarar makamashi a duniya.

A ranar Lahadi, Hukumar Tsaron Jiragen Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce an kai wa wata tankar ɗanyen mai hari da wani makami da ba a gano ko menene ba kusa da iyakar Oman.

Sai dai hukumar ta ce ma’aikatan jirgin suna cikin aminci kuma ba a samu rahoton gurɓatar muhalli ba.

Rahoton UKMTO ya ce hukumomi na binciken lamarin, yayin da aka shawarci sauran jiragen ruwa da ke ratsa yankin su ƙara taka-tsantsan.

Araghchi ya ce idan Amurka ta ɗauki matakin soja, Iran za ta “kare kanta da ƙarfi fiye da da”, yana mai cewa Tehran ba za ta amince a warware rikicin ta hanyar matsin lamba kawai ba.

A cewarsa, tattaunawa ce za ta iya samar da hanyar da za a cimma matsaya ta ƙarshe kan rikicin da kuma batutuwan da suka shafi Mashigar Hormuz.

Continue Reading
You may also like...

More in

Recent Post

Advertisement Enter ad code here

Facebook

Headlines

To Top