Connect with us

Firstpost

Ebola ta hallaka sama da mutane dubu 4 a Congo

Ebola ta hallaka sama da mutane dubu 4 a Congo

Hukumomin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo sun ce cutar Ebola ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 4, daga cikin sama da mutane dubu 8 da suka kamu da cutar.

A cewar wasu alƙaluma da hukumomin ƙasar suka fitar, mutane dubu 4 da 18 ne suka mutu daga cikin mutane dubu 8 da ɗari 3 da suka kamu da cutar, sannan wasu dubu 2 da ɗari 162 suka warke daga jinyar da suka yi.

Annobar wacce a hukumance aka fara sanar da ɓullarta a tsakiyar watan Mayu, ta shafi yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula a ƙasar ta tsakiyar Afirka, lamarin da ke kawo cikas ga ƙoƙarin shawo kan balahirar cutar a ƴan kwanakin nan.

Bayan ɓarkewar cutar a yankin Ituri, wanda ke arewa maso gabashin ƙasar, yanzu ta sake bazuwa larduna bakwai a yankunan arewa da gabashi.

Ayyukan shawo kan cutar da ake yi na fuskantar koma baya sakamakon rikice-rikice da kuma yadda al’ummar yankunan basu amince da hukumomi ba.

Continue Reading
You may also like...

More in

Recent Post

Advertisement Enter ad code here

Facebook

Headlines

To Top