Duk mai muƙamin da ke jin bai amfana da gwamnatina ba ya yi murabus — Lawal
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buƙaci masu riƙe da muƙamin siyasa da ke ganin ba sa amfana da gwamnatinsa da su yi murabus.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gusau.
- Iran ta ce ƙarfin soji ba zai kawo wa Amurka mafita ba
- ’Yan bindiga sun bai wa iyalan masu yi wa ƙasa hidima wa’adin biyan N1bn kuɗin fansa
Lawal ya yi wannan bayani ne yayin da wasu masu riƙe da muƙamin siyasa, matasa da mata ke ƙorafin cewa ba sa samun kulawa daga gwamnatinsa.
“Akwai wasu masu riƙe da muƙaman siyasa da ke cewa ba su samu komai ba. Wannan ba gaskiya ba ne. Ko a cikin kwamishinoni, duk wanda yake ganin ba ya samun komai, ya yi murabus,” in ji shi.
Gwamnan ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen samar da ababen more rayuwa da sauran ayyukan ci gaba a faɗin jihar.
Ya ce bayanai sun nuna cewa an gudanar da ayyukan more rayuwa da suka haura Naira biliyan 20 a kowace daga cikin Ƙananan Hukumomi jihar 14 cikin shekaru uku.
Lawal, ya ce bayan shekaru uku yana mayar da hankali kan mulki, ayyukan raya ƙasa da samar da zaman lafiya, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan harkokin siyasar jam’iyya.
“Tsawon shekaru uku mun mayar da hankali kan mulki. Yanzu lokaci ya yi da za mu koma harkokin siyasa, domin lokacinsa ya yi,” in ji Lawal.
Gwamnan ya amince cewa kuskuren da gwamnatinsa ta yi shi ne rashin bayyana sunayen mutanen da aka bai wa kwangiloli. Ya ce za a fitar da sunayen nan ba da jimawa ba.
Haka kuma, Lawal ya yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da su haɗa kai tare da kawo ƙarshen ɓangaranci.
“Daga yau, don Allah mu daina siyasar gidan wane da gidan wane. Mu haɗa kai a matsayin jam’iyya ɗaya mai manufa guda,” in ji shi.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta horas da matasa aƙalla 3,000 a fannoni daban-daban, sannan tana taimaka wa waɗanda suka kammala karatu domin su dogara da kansu.
Ya kuma ce zai gana da tsoffin gwamnonin jihar, Ahmad Yarima, Mamuda Shinkafi, Abdulaziz Yari da Bello Matawalle, a Abuja domin tattaunawa kan waɗanda za su kasance cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a Zamfara.
Lawal, ya tabbatar wa ’yan jam’iyyar cewa ya saurari ƙorafe-ƙorafensu kuma gwamnati za ta samar da tsare-tsare domin tabbatar da cewa mutane da dama sun amfana.
“An rubuta dukkanin ƙorafe-ƙorafen. Na ji su kuma na ɗauki bayaninsu. Za mu samar da tsare-tsare domin kowa ya amfana, in Allah ya so,” in ji shi.