An daƙile harin ’yan bindiga a Sakkwato
’Yan sanda a Jihar Sakkwato sun daƙile wani hari da ake zargin ’yan bindiga sun kai ƙauyen Tsabre da ke Ƙaramar Hukumar Isa, inda suka ƙwato makaman harba roka guda biyu.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar 2 ga Oktoba, lokacin da wasu ɗauke da makamai suka shiga ƙauyen suka buɗe wa mazauna wuta, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici.
- Tinubu zai ƙaddamar da shirye-shiryen rage tsadar rayuwa a makonni masu zuwa
- Ebola ta hallaka sama da mutane dubu 4 a Congo
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i, ya ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun isa yankin bayan rundunar ta samu kiran neman agaji.
Ya ce jami’an sun yi musayar wuta da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa wani daji da ke kusa.
Rufa’i ya ce daga baya jami’an tsaron sun gudanar da sintiri a yankin, inda suka tsinto makaman harba roka guda biyu da aka bari a wurin.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko an samu asarar rayuka ko raunuka tsakanin mazauna ƙauyen, jami’an tsaro ko maharan ba.
Hakan na zuwa ne yayin da hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da addabar wasu sassan jihar Sakkwato da sauran jihohin Arewa maso Yamma.