A kawo mana shanu 700 da tumaki 1000 — ’Yan bindiga
An ba da rahoton cewa, sama da unguwanni uku a Karamar Hukumar Kankia sun fice daga gidajensu biyo bayan wasu wasiƙu da ’yan bindiga suka aikowa unguwannin Rimaye da Sukunturi a Jihar Katsina.
A cikin wasiƙun, ’yan bindigar sun buƙaci al’ummomin unguwannin da su ba su shanu 700 da tumaki 1,000 domin kaucewa kai musu hari.
A cewar wani mazaunin yankin Kankia, Malam Ahmadu Kankia, ’yan bindigar sun isar da wasiƙun ne a ranar 6 ga watan Afrilu, 2026, inda suka sanya ranar Juma’a, 10 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe ta cika wa’adin wannan sharaɗi.
Ya bayyana cewa barazanar ta haifar da firgici da tsoro, wanda hakan ya sa mazauna ƙauyukan Kunduru, Sukunturi, Tsa da Magam ficewa daga gidajensu tun kafin wa’adin ya cika.
“An aika wasiƙun daban-daban zuwa Rimaye da Sukunturi, amma abin da ke ciki ɗaya ne. Sun buƙaci unguwannin su samar da shanu 700 da tumaki 1,000 cikin kwanaki huɗu. Mutane sun tsorata kuma suka fara yin ƙaura. Yayin da nake magana yanzu, waɗannan al’ummomi duk sun fice; kowa ya gudu,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin, Usman Dada, ya bayyana cewa an rubuta wasiqun ne da Turanci, sannan ya ƙara da cewa dukkan mambobin al’ummar sun yanke shawarar komawa wurare masu aminci, musamman cikin garin Kankia, don tsoron kada a kai musu hari idan suka ci gaba da zama a ƙauyukansu.
An kuma bayar da rahoton cewa, ’yan kwanakin nan, wasu mazauna ƙauyukan da abin ya shafa sukan taru a ƙungiyance da rana don kwashe ragowar dabbobinsu daga qauyukan da suka bari, ganin cewa yawancin hare-hare kan faru ne ko dai da sassafe ko kuma da yamma.
“Sukan tafi rukuni-rukuni su kwashe ragowar dabbobinsu, waɗanda suke kawowa kasuwa don sayarwa. Kauyukansu yanzu sun zama kango, kuma babu wanda ke son komawa a halin yanzu,” in ji wata majiya daga yankin.