Connect with us

Firstpost

Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi

Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi

Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene.

Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a jihar, inda suke ci gaba da samun kulawa.

Kwamishinan Harkokin Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce wannan hatsari abun baƙin ciki ne ga gwamnati da jama’a.

Ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya umarci gwamnatin jihar da ta biya dukkanin kuɗin maganin waɗanda suka jikkata kuma ta tura jami’ai zuwa asibitoci don tallafa wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.

Fanwo ya ce: “Gwamnatin Jihar Kogi tana jimami sosai tare da iyalan waɗanda suka rasu guda shida, kuma za ta tallafa musu.”

Continue Reading
You may also like...

More in

Recent Post

Advertisement Enter ad code here

Facebook

Headlines

To Top