Connect with us

Firstpost

Har yanzu ba a gama da Boko Haram ba — Inuwa Yahaya

Har yanzu ba a gama da Boko Haram ba — Inuwa Yahaya

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce duk da raunana ƙarfin Boko Haram da aka yi, amma har yanzu ƙungiyar na kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.

Gwamnan ya ce rashin tsaro na ci gaba da hana wasu mutanen da suka rasa matsugunansu komawa gidajensu, yayin da yara da dama ke ci gaba da zama ba tare da zuwa makaranta ba.

Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), ya bayyana hakan ne a taron Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) karo na 13 da aka gudanar a Maiduguri ranar Asabar.

“An raunana Boko Haram, amma ba a gama da su ba. Har yanzu muna ganin ana kai hare-hare kan al’ummominmu,” in ji shi.

Ya ce bayan Boko Haram, ayyukan ’yan bindiga da rikice-rikicen al’umma na ƙara zama barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.

Gwamnan ya ce matsalar tsaron ta kuma ƙara ta’azzara matsalolin jinƙai, ilimi da kiwon lafiya, musamman yadda wasu yara ke ci gaba da zama ba sa zuwa makaranta.

Ya ce akwai buƙatar gwamnatocin yankin su haɗa ƙarfi wajen magance matsalolin da suka shafi tsaro, laifuffukan da suka ratsa iyakokin jihohi, ƙarancin makamashi da sauran matsalolin jinƙai.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda aka gaza kammala wasu manyan ayyukan raya yankin, ciki har da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla, haɗa yankin da layin dogo da faɗaɗa hanyoyin sadarwar intanet mai sauri.

Ya tunatar da cewa an kafa NEGF a Gombe a watan Maris na 2020 domin bai wa gwamnonin yankin damar tunkarar matsalolin da suka fi ƙarfin kowace jiha magancewa ita kaɗai.

Sai dai ya ce an samu wasu nasarori a fannonin tsaro, ababen more rayuwa, samar da wutar lantarki, bunƙasa tattalin arziki da haɓaka ƙwarewar jama’a.

Gwamnan ya kuma bayyana aikin haƙo man fetur na Kolmani a matsayin babbar dama ga Arewa maso Gabas, yana mai cewa ya kamata a tabbatar da cewa an mayar da albarkatun yankin zuwa samar da ayyukan yi da kuɗaɗen shiga.

Ya yi gargaɗin cewa dole ne a sarrafa ma’adinan yankin bisa ƙa’ida domin amfanin jama’a, maimakon su zama hanyar samun kuɗin tallafa wa aikata laifuka da ta’addanci.

“Dole ne mu kasance masu gaskiya ga kanmu da kuma al’ummarmu. Matsalolin da muka sa a gaba domin magancewa a shekarar 2020 har yanzu ba su gushe ba,” in ji shi.

Taron na Maiduguri ya kuma mayar da hankali kan nazarin nasarorin da aka samu da kuma ƙalubalen da har yanzu ke fuskantar yankin, da kuma shirin miƙa ragamar jagoranci ga waɗanda za su gaje su.

Gwamnonin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe da Yobe, waɗanda suka kafa ƙungiyar, ana sa ran za su kammala wa’adin mulkinsu na shekaru takwas a watanni masu zuwa.

Continue Reading
You may also like...

More in

Recent Post

Advertisement Enter ad code here

Facebook

Headlines

To Top