’Yan bindiga sun bai wa iyalan masu yi wa ƙasa hidima wa’adin biyan N1bn kuɗin fansa
’Yan bindigar nan da suka yi garkuwa da wasu matasa masu yi wa ƙasa hidima kimanin 20 a Jihar Oyo, sun bai wa iyalansu wa’adin sa’o’i 24 su biya kuɗin fansa na Naira biliyan ɗaya domin su sake su.
Iyalan matasan sun ce masu garkuwar sun nemi fansar Naira miliyan 50 kan kowane mutum, lamarin da ya kai jimillar kuɗin zuwa Naira biliyan ɗaya ke nan.
- An daƙile harin ’yan bindiga a Sakkwato
- Tinubu zai ƙaddamar da shirye-shiryen rage tsadar rayuwa a makonni masu zuwa
Sun bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da suka ziyarci Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, a gidansa da ke Bodija, Ibadan, tare da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Oyo, Olugbenga Abimbola, da Aseyin na Iseyinland, Oba Sefiu Adeyeri.
Iyalan sun ce masu garkuwar sun tuntuɓe su ne ta wayoyin ’ya’yansu da aka sace, inda suka yi barazanar cutar da su idan ba a biya kuɗin cikin wa’adin da suka sanya ba.
Da suke magana a madadin iyalan, Alhaja Alimot Akande da Oyebola Michael Akande sun roƙi Olubadan da ’yan sanda su taimaka wajen ganin an kuɓutar da matasan cikin gaggawa.
“Sai faman kiranmu suke yi suna neman Naira miliyan 50 a kan kowane mutum. Suna barazanar cewa wani abu mara kyau zai faru da ’ya’yanmu idan ba mu biya ba.
“Babu yadda za mu iya tara irin wannan kuɗi a wannan lokaci. Baba, muna roƙon ka taimaka mana. Kada su kashe ’ya’yanmu,” in ji su.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce ’yan bindigar suka yi awon gaba da matasan waɗanda ke kan hanyarsu daga Ibadan zuwa sansanonin yi wa ƙasa hidima na NYSC da ke Jihohin Abia da Akwa Ibom, bayan sun tare motocin bas biyu da suke ciki a yankin Umunoha da ke kan titin Owerri zuwa Onitsha.
A halin da ake ciki, Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya tura Mataimakin Sufeto-Janar mai kula da ayyuka, Shehu Nadada, da wasu kwamishinonin ’yan sanda zuwa Jihar Imo domin jagorantar aikin ceto matasan.
Rundunar ta kuma ƙara tura jami’an dabaru da kayan aiki domin ƙarfafa aikin neman matasan da kuma sauran mutanen da aka sace.
Kwamishinan ’Yan Sandan Oyo, Abimbola, ya ce ya tuntuɓi takwaransa na Imo tun bayan faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace cikin aminci.
Olubadan Ladoja ya kuma tabbatar wa iyalan cewa za a yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ’ya’yansu cikin ƙoshin lafiya.